Leviticus 27:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada kuwa ya zaɓa mai kyau daga marar kyau, ko yă yi musaya. In ya yi musaya kuwa, dabbar da wadda ya musayar, za su zama masu tsarki, ba kuma za a fanshe su ba.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاعَ ذَاٻِ دَبَّرْ تَغُواْمَ عَكَنْ ݣَنْتَ كُواْ رَشِنْ ݣَنْتَ بَ، بَ كُوَ ذَاعَ يَرْدَ عَثَنْجَتَبَ؞ عِدَنْ أَنْثَنْجَ دَبَّ دَ وَتَ، تُواْ، دُكَ بِيُنْ دَ عَكَ ثَنْجَ ذَاسُ كَسَنْثٜىٰ مَاسُ ڟَرْكِے؞ بَذَاعَ عِيَ ڢَنْسَرْسُبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.