Leviticus 4:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘In dukan jama’ar Isra’ilawa suka yi zunubi ba da gangan ba, har suka aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake jama’ar ba su san batun ba, duk da haka sun yi laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ دُكَنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ نٜىٰ سُنْيِ ذُنُوبِ بَ دَ غَنْغَنْبَ، حَرْ تَارُوانْ جَمَعَرْ بَسُ سَنِ بَ، سُكَ كَرْيَ طَيَ دَغَ ثِكِنْ دُواْكُواْكِنْ يَهْوٜىٰهْ ، وَنَّنْ يَجَٰوُاْ مُسُ لَيْڢِے كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan taron jama'ar Isra'ila sun yi zunubi, ba da gangan ba, har sun aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, amma ba su farga da laifinsu ba, duk da haka sun yi laifi.