Leviticus 4:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai zuba jinin a ƙahonin bagaden da suke gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. Zai zuba sauran jinin a gindin bagaden hadaya ta ƙonawa a ƙofar zuwa Tentin Sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طِبِے جِنِنْ يَسَا عَڧَهُواْنِنْ بَغَدٜىٰنْ وَنْدَ يَكٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ عَثِكِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ؞ سَوْرَنْ جِنِنْ ذَيْ ظُبَ أَغِنْدِنْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا وَنْدَ يَكٜىٰ عَڧُواْڢَرْ شِغَ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ɗiba daga cikin jinin ya shafa wa zankayen bagaden da suke cikin alfarwa ta sujada a gaban Ubangiji, sauran jinin kuwa sai ya zuba a gindin bagaden ƙona hadaya wanda yake a ƙofar alfarwa ta sujada.