Leviticus 4:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsarsa yă sa a ƙahonin bagaden hadayar ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a gindin bagade.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْ طِبَ جِنِنْ دَ يَڟَرْسَ يَسَا عَڧَهُواْنِنْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا؞ سَوْرَنْ جِنِنْ ذَيْ ظُبَ أَغِنْدِنْ بَغَدٜىٰ نَهَدَايَ تَڧُواْنَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai firist ya ɗibi jinin hadaya don zunubi da yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden ƙona hadaya, sa'an nan ya zuba sauran jinin a gindin bagaden.