Leviticus 5:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Firist zai miƙa ɗayan matsayin hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka tsara, yă kuma yi kafara dominsa saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta masa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَبِيُنْ كُمَ ذَيْ مِيڧَ شِ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا بِسَغَ ڧَٰعِدُواْدِنْ دَ عَكَ بَايَرْ؞ تَهَكَ ڢِرِسْتِ ذَيْ طَوْكِ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ دُواْمِنْ ذُنُوبِنْ دَ مُتُمِنْ يَيِ، ذَاعَ كُوَ غَاڢَرْتَا مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan zai miƙa ta biyun don hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka ƙayyade. Firist ɗin zai yi kafara saboda laifin da mutumin ya yi, za a kuwa gafarta masa.