Leviticus 5:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘In ba zai iya kawo kurciyoyi biyu ko tattabarai biyu ba, sai yă kawo humushin garwan gari mai laushi domin hadaya don zunubi. Ba lalle ba ne yă sa mai ko turare a kansa, saboda wannan hadaya ce ta zunubi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا عِدَنْ بَذَيْ عِيَ كَٰوُاْ كُرْثِيُواْيِ بِيُ كُواْ یَنْ تَتَّبَرُ بِيُ بَ، تُواْ، سَيْ يَكَٰوُاْ كِلُواْ طَيَ نَغَارِنْ حَڟِ مَيْ لَوْشِ دُواْمِنْ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِنْدَ يَعَيْكَتَ؞ بَذَيْسَا مَيْ كُواْ تُرَارٜىٰ عَكَيْبَ، غَمَا هَدَايَ ثٜىٰ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ بَ هَدَايَ تَهَڟِ بَ ثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.