Leviticus 5:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole yă biya abin da ya kāsa yi dangane da abubuwa masu tsarki, yă ƙara kashi ɗaya bisa biyar na darajar abin a kan wannan sa’an nan yă ba wa firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمِنْ ذَيْبِيَ سَبُواْدَ أَبِنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے وَنْدَ مُتُمِنْ يَيِ لَيْڢِے عَكَنْسَ؞ ذَيْ كُمَ ڧَارَ كَشِ طَيَ ثِكِنْ بِيَرْ عَكَيْ، يَبَا ڢِرِسْتِ؞ ڢِرِسْتِ كُوَ ذَيْ طَوْكِ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِنْسَ تَوُرِنْ مِيڧَ ضَغُواْ هَدَايَ تَشَاڢٜىٰ لَيْڢِے، ذَاعَ كُوَ غَاڢَرْتَا مَسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai kuma biya diyya saboda abu mai tsarki da ya yi laifi a kansa. Zai kuma ƙara humushi a kai, sa'an nan ya ba firist. Firist kuwa zai yi kafara dominsa da ragon hadaya don laifi. Za a kuwa gafarta masa.