Leviticus 5:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Ko kuwa in mutum ya taɓa wani abin da yake mai ƙazanta, ko gawar naman jeji marar tsabta, ko na shanu marar tsabta, ko na halittu marasa tsabtan da suke motsi a ƙasa; ko da yake bai sani ba, ya ƙazantu ke nan, kuma ya yi laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كُواْ كُوَ عِدَنْ مُتُمْ يَتَٻَ وَنِ أَبِنْ ڧَظَنْتَا نٜىٰ، بَ دَ سَنِنْسَبَ، كَمَرْ مُوشٜىٰنْ نَامَنْ دَاجِ مَيْ ڧَظَنْتَا، كُواْ مُوشٜىٰنْ دَبَّرْ غِدَا مَيْ ڧَظَنْتَا، كُواْ مُوشٜىٰنْ حَلِتُّو مَاسُ رَرَّڢٜىٰ، يَڧَظَنْتُ كٜىٰنَنْ؞ وَنَّنْ يَجَٰوُاْ مَسَ لَيْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko kuma idan mutum ya taɓa kowane abin da yake haram ko mushen haramtacciyar dabba ta jeji ko ta gida, ko mushen haramtaccen abin da yake rarrafe, zai zama da laifi, ko da bai sani ba.