Leviticus 5:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko kuwa in mutum bai yi tunani ba, ya yi rantsuwar yin wani abu, ko mai kyau ko marar kyau; ko da yake bai sani ba, duk da haka sa’ad da ya gane zai zama mai laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عِدَنْ مُتُمْ يَيِ سَوْرِنْ طَوْكَرْ ضَنْڟُوَا دَ بَاكِنْسَ عَكَنْ وَنِ أَبُ، بَاتَرٜىٰدَ يَيِ تُنَانِ تُكُنَبَ، كُواْ دَ أَبِنْ مَيْݣَوْ كُواْ مَرَرْ ݣَوْ نٜىٰ، بَاتَرٜىٰدَ سَنِنْسَبَ دَظَرَرْ يَغَانٜىٰ، تُواْ، وَنَّنْ يَجَٰوُاْ مَسَ لَيْڢِے كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko kuma idan mutum ya yi rantsuwa da garaje da bakinsa, cewa, zai yi mugunta, ko nagarta, ko kowace irin rantsuwa ta garaje da mutane sukan yi, to, laifi ya kama shi bayan da ya gane da rantsuwarsa.