Leviticus 6:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan firist zai sa rigunarsa ta lilin da kuma rigar lilin da ake sa a ciki, sa’an nan yă kwashe tokan hadaya ta ƙonawa da wuta da ta ci a kan bagaden, yă sa kusa da bagaden.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِرِسْتِ ذَيْسَا رِيغُنَنْسَ نَلِيلِنْ دَ غَجٜىٰرٜىٰنْ وَنْدُواْ؞ ذَيْ ݣُوشِ تُواْكَرْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا يَسَا أَغٜىٰڢٜىٰنْ بَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Firist zai sa rigarsa ta lilin, ya ɗaura mukurunsa na lilin, sa'an nan ya kwashe tokar hadaya ta ƙonawa daga bagaden, ya zuba a gefensa.