Leviticus 6:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haruna da ’ya’yansa maza za su ci sauran, amma za a ci shi ba tare da yisti ba a tsattsarkan wuri; za su ci shi a harabar Tentin Sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِنْ دَ يَرَغُ دَغَ هَدَايَ تَهَڟِنْ ذَيْ ذَمَ رَبُواْ نَڢِرِسْتِنٜىٰ، وَتُواْ هَٰرُونَ دَ یَیَنْسَ مَظَا؞ ذَاسُثِ شِ بَابُ يِسْتِ أَوَنِ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے عَثِكِنْ ڢِيلِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haruna da 'ya'yansa maza za su ci ragowar garin. Za a ci shi ba tare da yisti ba a wuri mai tsarki na farfajiyar alfarwa ta sujada.