Leviticus 6:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk wanda aka naɗa daga ’ya’yan Haruna yă zama firist a madadinsa, shi ne zai miƙa wannan hadayar ga Ubangiji. Zai ƙone hadayar ƙurmus. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce har abada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ دُكْ وَنْدَ عَكَ نَطَشِ يَغَاجِ مَڟَيِ نَبَبَّنْ ڢِرِسْتِ دَغَ یَیَنْ هَٰرُونَ، شِينٜىٰ ذَيْ مِيڧَ وَنَّنْ هَدَايَ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَاعَڧُواْنَ هَدَايَرْ دُكَ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ تَدِنْدِنْدِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.