Leviticus 6:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma duk wata hadaya don zunubi wadda aka kawo jininta cikin Tentin Sujada don a yi kafara a Wuri Mai Tsarki, ba za a ci ba. A maimako haka za a ƙone ta ɗungum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ أَنْطِبَ جِنِ دَغَ هَدَايَ تَوَنْكٜىٰ ذُنُوبِ، أَنْشِغَرْ دَشِ ثِكِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ دُواْمِنْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، بَذَاعَثِ نَامَنْ هَدَايَرْ بَ؞ ذَاعَڧُواْنٜىٰشِ دَ وُتَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ba za a ci naman hadaya don zunubi ba wanda aka shigar da jininsa a alfarwa ta sujada domin yin kafara a Wuri Mai Tsarki. Sai a ƙone shi da wuta.