Leviticus 7:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘In ya miƙa hadayar a matsayin hadaya ta godiya ce, to, zai miƙa ta tare da burodi mai kauri marar yisti, wanda aka kwaɓa da mai, da burodi marar kauri, wanda aka shafa wa mai, da kuma burodi mai kauri da aka yi da gari mai laushi wanda aka kwaɓa sosai da mai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ مُتُمْ يَمِيڧَ هَدَايَرْ سَبُواْدَ غُواْدِيَ، تُواْ سَيْ يَمِيڧَ دَبَّرْ هَدَايَرْ تَرٜىٰدَ وَيْنَ مَرَرْ يِسْتِ وَدَّ عَكَ ݣُوٻَ دَ مَيْ دَ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ وَنْدَ عَكَ شَاڢَ دَ مَيْ دَ كُمَ وَيْنَ تَغَارِ مَيْ لَوْشِ وَنْدَ يَشَا مَيْ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan domin godiya mutum ya miƙa hadaya, sai ya miƙa ta tare da abinci marar yisti, wadda aka kwaɓa da mai, da wadda aka shafa wa mai, da kuma ƙosai.