Leviticus 7:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘In hadayarsa cika wa’adin rantsuwa ce ko kuwa ta yardar rai ce, sai a ci hadayar a ranar da ya miƙa ta, amma za a iya cin duk abin da ya rage kashegari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا عِدَنْ دُواْمِنْ ثِكَ ضَنْڟُوَا نٜىٰ مُتُمْ يَكَٰوُاْ هَدَايَ تَسَامُنْ سَلَمَ، كُواْ دُواْمِنْ بَايَرْوَ تَيَرْدَرْ رَيْ، ذَاعَ عِيَ ثِنْ نَامَنْ أَ رَانَرْ دَ عَكَ مِيڧَ هَدَايَرْ، كُمَ أَبِنْدَ يَرَغُ ذَاعَ عِيَ ثِنْ شِ وَشٜىٰغَرِ كُواْ دَ يَݣُونَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan hadayarsa ta cika wa'adi ce, ko ta yardar rai ce, sai a ci ta a ranar da aka miƙa ta, kashegari kuma a ci abin da ya ragu.