Leviticus 7:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami albarkar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci kuwa ya yi laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ أَنْثِ نَامَنْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ أَ رَانَ تَ عُكُ، تُواْ يَهْوٜىٰهْ بَذَيْ كَرْٻَ بَ، بَذَيْ لِسَّڢْتَا هَدَايَرْ مُتُمِنْدَ يَكَٰوُاْ تَ وَنِ أَبُبَ؞ نَامَنْ ذَيْ ذَمَ أَبِنْ ڨَمَ، كُمَ دُكْ وَنْدَ يَثِ نَامَنْ يَجَٰوُاْ وَكَنْسَ لَيْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan aka ci naman hadayarsa ta salama a rana ta uku, ba za a karɓi wanda ya ba da hadayar har ya sami fa'idar hadayar ba, naman zai zama abin ƙyama, duk wanda ya ci ya yi laifi.