Leviticus 8:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Musa ya yanka bijimin ya ɗauki jinin, ya sa yatsarsa ya zuba a dukan ƙahonin bagade don yă tsarkake bagaden. Ya zuba sauran jinin a gindin bagade. Ta haka ya tsarkake shi don yă yi kafara dominsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ كُوَ يَنْكَشِ؞ مُوسَٰى يَطِبِے جِنِنْ دَ يَڟَرْسَ يَشَاڢَ عَكُواْوَنٜىٰ ڧَهُوانْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ دُواْمِنْ أَڟَبْتَثٜىٰ بَغَدٜىٰنْ؞ سَيْ يَظُبَ جِنِنْ أَغِنْدِنْ بَغَدٜىٰنْ؞ تَهَكَ يَكٜىٰٻٜىٰشِ دَ ڟَرْكِے يَكُمَ ڟَبْتَثٜىٰشِ دُواْمِنْ أَ عِيَيِنْ هَدَايَ عَكَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Musa ya yanka shi, ya ɗibi jinin a yatsansa ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye, ya tsarkake bagaden, ya zuba jinin a gindin bagaden, ya keɓe shi don ya yi kafara dominsa.