Leviticus 8:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Musa kuwa ya yanka ɗan ragon ya ɗibi jinin ya sa leɓatun kunnen dama na Haruna, ya kuma sa a babbar yatsarsa ta hannun dama da kuma a babbar yatsar ƙafarsa ta dama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ كُوَ يَنْكَ شِ؞ سَيْ مُوسَٰى يَطِبِے جِنِنْ يَسَا أَ لٜىٰٻٜىٰنْ كُنّٜىٰنْ دَامَ نَ هَٰرُونَ دَ بَبَّرْ يَڟَرْسَ تَهَنُّنْ دَامَ دَ بَبَّرْ يَڟَرْسَ تَڧَڢَرْ دَامَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Musa kuwa ya yanka shi, ya ɗibi jinin, ya sa a leɓatun kunnen dama na Haruna, da bisa babban yatsansa na hannun dama, da babban yatsa na ƙafar dama.