Leviticus 8:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُوسَٰى يَثِرٜىٰ كِڟٜىٰنْ ضَغُوانْ دَ كِڟٜىٰنْ وُڟِيَرْ دَ دُكَنْ كِڟٜىٰنْدَ يَرُڢٜىٰ كَايَنْ ثِكِ دَ سَاشٜىٰ مَڢِے ݣَوْ نَهَنْتَ دَ ڧُواْدَ بِيُنْ تَرٜىٰدَ كِڟٜىٰنْسُ دَ كُمَ ثِنْيَرْ دَامَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ɗauki kitsen, da wutsiya mai kitse, da dukan kitsen da yake bisa kayan ciki, da matsarmama da ƙodoji biyu da kitsensu, da cinyar dama.