Leviticus 8:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ ثِكِنْ ݣُونْدُوانْ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ وَنْدَ يَكٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ يَطَوْكِ دُنْڧُلٜىٰ طَيَ نَغُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ دَ دُنْڧُلٜىٰ طَيَ نَغُرَاسَرْ دَ عَكَ ݣُوٻَ دَ مَيْ دَ كُمَ بِسْكِتْ طَيَ، يَسَاسُ عَكَنْ كِڟٜىٰنْ دَ ثِنْيَرْ دَامَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga cikin kwandon abinci marar yistin da yake a gaban Ubangiji, ya ɗauki waina guda marar yisti, da waina guda da aka yi da mai, da ƙosai guda. Sai ya ɗibiya su a bisa kitsen da cinyar dama.