Leviticus 8:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku bar ƙofar Tentin Sujada har kwana bakwai, sai ranakun naɗi suka cika, gama naɗinku zai ɗauki kwana bakwai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاكُ ڢِتَ وَجٜىٰ دَغَ ڧُواْڢَرْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ بَ، سَيْ بَايَنْ ݣُونَ بَݣَويْ، وَتُواْ سَيْ كُنْ ثِكَ ݣُونَكِنْ ڧَٰعِدَرْ نَطَوَرْكُ، غَمَا ڧَٰعِدَرْ نَطَوَرْكُ ذَاتَ طَوْكِ ݣُونَ بَݣَويْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za ku fita daga cikin alfarwa ta sujada ba har kwana bakwai, wato, sai kwanakin keɓewarku sun cika, gama keɓewarku za ta ɗauki kwana bakwai.