Leviticus 9:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haruna ya yanka maraƙin da ragon a matsayin hadaya ta salama domin mutane. ’Ya’yansa maza suka miƙa masa jinin, ya kuwa yayyafa shi a kowane gefe na bagade.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ حَكَ سَيْ هَٰرُونَ يَيَنْكَ بِجِمِنْ دَ ضَغُوانْ دُواْمِنْ هَدَايَ تَڠَرَنْ زُمُنْثِ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْ؞ سَيْ یَیَنْسَ سُكَ كَٰوُاْ مَسَ جِنِنْ، سَيْ يَيَيَّڢَا شِ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ بَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.