Luke 1:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ زَكَرِيَّا يَثٜىٰ وَمَلاَىِٕكَنْ «يَيَ ذَنْسَنْ ثٜىٰوَ أَبِنَّنْ دَكَڢَطِ حَكَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ؟ غَانِ نَا ڟُوڢَ، عُوَرْغِدَانَ كُمَ تَنَ شٜىٰكَرُ مَاسُيَوَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Zakariya ya ce wa mala'ikan, “Ta ƙaƙa zan san haka? Ga ni tsoho, maiɗakina kuma ta kwana biyu.”