Luke 11:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranar shari’a, Sarauniyar Kudu za tă tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ شَرِيعَ، سَرَوْنِيَرْ شٜىٰبَ ذَاتَ تَاشِ تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ زَامَانِنَّنْ تَنُونَ مُسُ بَسُيِ دَيْدَيْبَ، غَمَا تَاذُواْ نٜىٰ دَغَ وُرِے مَيْ نِيسَ سُواْسَيْ دُوانْ تَجِ كُواْيَرْوَرْ حِكِمَرْ سُلَيْمَٰنُ؞ عَمَّا غَ وَنْدَ يَڢِ سُلَيْمَٰنُ أَنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan ta kā da su. Don ta zo ne daga bangon duniya tă ga hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.