Luke 11:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Idonka shi ne fitilar jikinka. Sa’ad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma sa’ad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدُواْ شِينٜىٰ ڢِتِلَرْ جِكِے؞ إِنْ عِدُوانْكَ يَنَ دَ لَاڢِيَ، دُكَنْ جِكِنْكَ ذَيْثِكَ دَ حَصْكٜىٰ؞ عَمَّا عِدَنْ عِدُوانْكَ بَا لَاڢِيَ، سَيْ دُكَنْ جِكِنْكَ يَرَسَ حَصْكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ido shi ne fitilar jiki. In idonka lafiyayye ne, duk jikinka zai cika da haske. In kuwa idonka da lahani, sai jikinka ya cika da duhu.