Luke 11:51 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتُواْ، تُنْدَغَ جِنِنْ هَبِيلَ حَرْ ذُوَا نَ زَكَرِيَّا، وَنْدَ عَكَ كَشٜىٰ ڟَكَانِنْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ دَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے ثِكِنْ هَيْكَلِ؞ عِ، إِنَ غَيَ مُكُ، ذَاعَ حُكُنْتَ مُتَنٜىٰنْ زَامَانِنَّنْ سَبُواْدَ وَطَنَّنْ دُكَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
wato, tun daga jinin Habila, har ya zuwa na Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagaden hadaya da Wuri Mai Tsarki. Hakika, ina gaya muku, duk za a bi shi kan mutanen wannan zamani.