Luke 12:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُدُوبِے يَدَّ سُو ڢُلَوَ سُكٜىٰ غِرْمَ مَنَ؞ بَاسَ عَيْكِ، بَاسَ سَاڧَرْ كُواْمٜىٰ، بَاسَيِ وَكَنْسُ رِيغُنَ، دُكْدَهَكَ إِنَ غَيَ مُكُ كُواْ سَرْكِے سُلَيْمَٰنُ دَ دُكَنْ غِرْمَنْسَ بَيْتَٻَيِنْ أَدُواْ كَمَرْ طَيَ دَغَ ثِكِنْسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku dubi dai furanni yadda suke girma, ba sa aikin fari, ba sa na baƙi, duk da haka, ina gaya muku, ko Sulemanu ma, shi da adonsa duk, bai taɓa yin adon da ya fi na ɗayansu ba.