Luke 12:53 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَابَ ذَيْ يِغَابَادَ طَنْسَ، طَنْ كُمَ يَيِ غَابَادَ بَابَنْسَ؞ مَامَا ذَاتَيِ غَابَادَ یَرْتَ، یَرْ كُمَ تَيِ غَابَادَ مَامَرْتَ؞ مَامَرْ مِجِ ذَاتَيِ غَابَادَ مَاتَرْ طَنْتَ، مَاتَرْ طَنْ كُمَ تَيِ غَابَادَ مَامَرْ مِجِنْتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta haka, za su rabu. Uba yana gāba da ɗansa, ɗan kuma yana gāba da ubansa, uwa tana gāba da 'ya tata, 'yar kuma tana gāba da uwa tata, suruka tana gāba da matar ɗanta, matar ɗan kuma tana gāba da suruka tata.”