Luke 13:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ كُوَ مُتَنٜىٰ شَا تَݣُوسْ طِنَّنْ دَ حَصُومِيَا تَڢَاطِ عَكَنْسُ أَ سِلُوَمْ، يَكَشٜىٰسُ، كُنَ ڟَمَّنِ سُنْڢِے دُكْ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ عُرُوشَلِيمَ ذُنُوبِ نٜىٰ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?