Luke 14:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عِيسَىٰ يَثٜىٰ وَوَنْدَ يَكِرَشِ «عِدَنْ كَكِرَا وَنِ دُوانْ ثِنْ عَبِنْثِ، كُواْ كَشِرْيَ بِكِ، كَدَ كَكِرَا أَبُواْكَنْكَ نٜىٰ كَوَيْ، كُواْ یَنْعُوَنْكَ، كُواْ دَنْغِنْكَ، كُواْ مَڨُوبْتَنْكَ مَاسُ أَرْزِڧِ، دُوانْ وَتَرَانَ ذَاسُ كِرَاكَ، سُو مَا؞ تَهَكَ ذَاسُ بِيَاكَ أَبِنْدَ كَيِ مُسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka.