Luke 16:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَيْ مَيْغِدَنْ يَيَبِے وَكِيلِنَّنْ مَرَرْ غَسْكِيَ سَبُواْدَ يَيِ وَيُواْ؞ غَمَا یَنْ زَامَانِ سُنْ عِيَ بِيدَ مُتَنٜىٰنْ زَامَانِنْسُ دَ وَيُواْ ڢِيٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ حَصْكٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai maigidan ya yaba wa wakilin nan marar gaskiya saboda wayonsa. Don 'yan zamani a ma'ammalarsu da mutanen zamaninsu, sun fi mutanen haske wayo.