Luke 17:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ رَانَرْ نَنْ ڢَا، وَنْدَ يَكٜىٰ كَنْ رُڢِنْ طَاكِ كَدَ يَسَوْكُواْ وَيْ ذَيْ ݣُوشِ كَايَنْسَ عَثِكِنْ غِدَا؞ حَكَ مَا دُكْ وَنْدَ يَجٜىٰ غُواْنَ، كَدَ يَكُواْمَ غِدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ran nan fa wanda yake kan soro, kayansa kuma na cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda yake gona, kada ya juyo.