Luke 17:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya amsa musu ya ce, “In kuna da bangaskiya da take ƙanƙani kamar ƙwayar mustad, kuna iya ce wa wannan itacen durumi, ‘Ka tumɓuke daga nan, ka dasu a cikin teku.’ Zai kuwa yi muku biyayya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُبَنْغِجِ يَأَمْسَ مُسُ يَثٜىٰ «عِدَنْ كُنَدَ بَنْغَسْكِيَ دَ تَكَيْ كُواْ دَ مِصَالِنْ ڨُويَرْ مَسْتَدْ، وَدَّ تَڢِے ڧَنْڧَنْتَ ثِكِنْ إِرِ دُكَ ذَاكُثٜىٰ وَوَنَّنْ بَبَّنْ إِتَاثٜىٰ، ‹كَبَرْ نَنْ، كَجٜىٰ كَڟَيَ عَثَنْ ثِكِنْ تٜىٰكُ!› ذَيْ كُمَبِے أَبِنْدَ كُكَثٜىٰ يَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce, “Da kuna da bangaskiya, ko da misalin ƙwayar mastad, da za ku ce wa wannan durumi, ‘Ka ciru, ka dasu cikin teku,’ sai kuwa ya bi umarninku.”