Luke 20:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ لُواْكَثِنْ غِرْبِنْ إِنَبِنْ يَيِ، سَيْ يَعَيْكِ وَنِ بَاوَنْسَ يَجٜىٰ وُرِنْ وَطَنَّنْ دَ سُكَ كَرْٻِ هَيَرْ غُواْنَرْ، يَكَرْٻُواْ مَسَ وَطَنْسُ یَیَنْ إِنَبِے دَغَ غُواْنَرْ؞ عَمَّا یَنْ هَيَرْ سُكَيِ مَسَ دُوكَ، سُكَ سَلَّمٜىٰشِ حَنُّ وُاْڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da kakar inabi ta yi, ya aiki wani bawansa a gun manoman nan su ba shi gallar garkar. Amma manoman suka yi masa dūka, suka kore shi hannu wofi.