Luke 22:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنٜىٰنٜىٰ يَڢِ غِرْمَ، شِے وَنْدَ يَذَوْنَ يَنَثِ نٜىٰ، كُواْ كُمَ شِے دَيَكٜىٰ كَيْ مَاسُ عَبِنْثِ؟ أَيْ، وَنْدَ يَذَوْنَ يَنَثِ نٜىٰ؞ عَمَّا غَاشِ إِنَ عَثِكِنْكُ كَمَرْ مَيْكَيْ عَبِنْثِنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wa ya fi girma? Wanda ya zauna cin abinci, ko kuwa mai hidimar? Ashe, ba wanda ya zauna cin abinci ba ne? Ga shi kuwa, ina a cikinku kamar mai hidima.