Luke 23:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سُواْجُواْجِ سُنَ تَڢِيَ دَ عِيسَىٰ، سَيْ سُكَ سَدُ دَ وَنِنْدَ عَكٜىٰثٜىٰ دَشِ سِيمَنْ، مُتُمِنْ سَيِرِنْ، يَنَ ذُوَا دَغَ ڧَوْيٜىٰ؞ سُكَ ثَڢْكٜىٰشِ، سُكَسَا مَسَ غِثِّيٜىٰ يَطَوْكَ يَبِے عِيسَىٰ عَبَايَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suna tafiya da Yesu yake nan, sai suka cafke wani, mai suna Saminu Bakurane, yana zuwa daga ƙauye, suka ɗora masa gicciye, yă ɗauka ya bi Yesu.