Luke 3:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَنَ رِڧٜىٰ دَ مَتَنْكَطِنْسَ، ذَيْ تَنْكَطٜىٰ حَڟِنْسَ، كُمَ يَتَتَّارَ أَلْكَمَرْسَ يَسَا ثِكِنْ ضُمْبُنْسَ؞ عَمَّا ذَيْ ڧُواْنَ يَايِنْ دَ وُتَرْ دَ بَعَ عِيَ كَشٜىٰوَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙwaryar shiƙarsa tana hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkama ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun sai ya ƙone shi a wuta marar mutuwa.”