Luke 5:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَسُ سَامِ حَنْيَبَ سَبُواْدَ يَوَنْ مُتَنٜىٰ؞ دَسُكَغَ بَابُ دَامَ، سَيْ سُكَ هَوْ كَنْ رُڢِنْ طَاكِنْ، سُكَ ٻَلّٜىٰ رُڢِنْ سُكَ سَوْكَرْ دَشِ دُكْ دَ تَبَرْمَرْ دَيَكٜىٰ ݣُونْثٜىٰ عَكَيْ، سُكَ أَجِيٜىٰشِ أَڟَكِيَرْ مُتَنٜىٰ أَغَبَنْ عِيسَىٰ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da suka kasa samun hanyar shigar da shi saboda taro, suka hau a kan soron, suka zura shi ta tsakanin rufin soron duk da shimfiɗarsa, suka ajiye shi a tsakiyar jama'a a gaban Yesu.