Luke 5:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowa ya yi mamaki, ya kuma yabi Allah. Suka cika da tsoro, suna cewa, “Mun ga abubuwan banmamaki yau.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْسُ سُكَ كَامَ بَاكِ سُنَ مَامَاكِ! ثِكٜىٰدَ ڟُواْرُواْ، سُكَ يَبِے اللَّهْ ، سُنَ ثٜىٰوَ «يَوْ مُنْ غَ أَبِنْ مَامَاكِ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka yi mamaki matuƙa, su duka, suka yi ta ɗaukaka Allah, tsoro kuma ya kama su, suka ce, “Yau mun ga al'ajabai!”