Luke 5:37 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuma ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In ya yi haka, sabon ruwan inabi zai farfashe salkunan, ruwan inabin yă zube, salkunan kuma su lalace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُمَ بَاوَنْدَ ذَيْ ظُبَ سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے عَثِكِنْ ڟُواْڢَڢِّنْ سَلْكُنَ؞ عِدَنْ يَا يِهَكَ، سَيْ سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے يَڢَرْڢَشٜىٰ سَلْكُنَنْ ضُوً إِنَبِنْ يَظُبٜىٰ سَلْكُنَ كُمَ سُلَلَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba kuma mai ɗura sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ma an ɗura, sai sabon ruwan inabin ya fasa salkunan, ya zube, salkunan kuma su lalace.