Luke 6:48 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِے كَمَرْ مُتُمْ نٜىٰ وَنْدَ دَ ذَيْ غِنَا غِدَنْسَ، سَيْ يَحَڧَ ڧَسَا دَ ظُرْڢِ، يَكُمَ كَڢَ تُوشٜىٰنْ غِنِنْ عَكَنْ دُوڟٜىٰ؞ دَ عَكَيِ أَمْبَلِيَرْ ضُوَ، سَيْ تَبُغِ غِدَنْ، عَمَّا بَتَ عِيَ غِرْغِظَ غِدَنْبَ، سَبُواْدَ أَنْ‌غِنَاشِ دَݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kamar mutum yake mai gina gida, wanda ya yi haƙa mai zurfi, har ya sa harsashin ginin a kan fā. Da aka yi rigyawa, sai ruwan kogi ya bugi gidan, amma bai iya girgiza shi ba, saboda an gina shi da aminci.