Luke 7:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna ya ce, “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَطَنْدَ يَحْيَى يَعَيْكَ سُكَ تَڢِے، سَيْ عِيسَىٰ يَڢَارَيِ وَتَارُوانْ مُتَنٜىٰ مَغَنَ غَمٜىٰدَ يَحْيَى، يَنَ ثٜىٰوَ «مٜىٰكُكَجٜىٰ غَنِ أَدَاجِ؟ كُنْجٜىٰ غَنِنْ دُواْغُوَرْ ثِيَوَرْ دَ إِسْكَ تَكٜىٰ كَطَوَ نٜىٰ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Baya jakadun Yahaya sun tafi, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?