Luke 7:44 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَدُوبِے مَثٜىٰنْ، يَثٜىٰ وَ سِيمَنْ «كَغَا مَثٜىٰنَّنْ؟ نَا شِغُواْ غِدَنْكَ، بَكَ بَانِ ضُوَ إِنْ وَنْكٜىٰ ڧَڢَاڢُنَبَ، عَمَّا تَوَنْكٜىٰ ڧَڢَاڢُنَ دَ هَوَيٜىٰنْتَ، تَكُمَ غُواْغٜىٰسُ دَ غَاشِنْ كَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta.