Luke 7:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عِيسَىٰ يَتَڢِے تَرٜىٰدَسُو؞ دَ يَيِكُسَدَ غِدَنْ، بَبَّنْ سُواْجَنْ رُواْمَنَّنْ يَعَيْكَ دَ وَطَنْسُ أَبُواْكَنْسَ سُغَيَوَ عِيسَىٰ «يَا مَيْغِرْمَ، كَدَ كَدَمٜىٰ كَنْكَ سَبُواْدَنِ! بَنْ مَا إِسَ حَرْ دَ ذَاكَ ذُواْ غِدَانَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya matso kusa da gidan, sai jarumin ɗin ya aiki aminansa wurinsa su ce masa, “Ya Ubangiji, kada ka wahalar da kanka. Ban ma isa har ka zo gidana ba.