Luke 7:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا نِے مَا عَڧَرْڧَشِنْ إِيكُوانْ وَنِ نَكٜىٰ، كُمَ دَ سُواْجُواْجِ عَڧَرْڧَشِنَ، نَكَنْثٜىٰ وَوَنَّنْ، ‹جٜىٰكَ،› سَيْيَجٜىٰ؞ وَنِ كُوَ إِنْ ثٜىٰ مَسَ، ‹ذُواْ،› سَيْ يَذُواْ؞ إِنْ نَثٜىٰ وَبَاوَنَ، ‹يِ أَبُ كَاظَا،› سَيْ يَيِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don ni ma a hannun wani nake, da kuma soja a hannuna, in ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai ya je, wani kuwa in ce masa, ‘Zo,’ sai ya zo, in ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai ya yi.”