Luke 8:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِرِنْ دَ سُكَ ڢَاطِ عَثِكِنْ ڧَيَ كُوَ، سُونٜىٰ ݣُوتَنْثِنْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَجِ، عَمَّا عَكْوَانَ عَتَاشِ، سَيْ دَامُوَرْ دُونِيَا دَ نٜىٰمَنْ أَرْزِڧِ دَ سُوانْ جِنْ دَاطِے يَسَا سُنْ كَاسَ بَادَ أَمْڢَانِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda suka fāɗi cikin ƙaya kuwa su ne waɗanda suka ji Maganar, amma a kwana a tashi, sai yawan taraddadin duniya, da dukiya, da shagalin duniya su sarƙe su, har su kasa yin amfani.