Luke 8:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«بَاوَنْدَ ذَيْ كُنَّ ڢِتِلَ يَطَوْكِ ݣُونُواْ يَرُڢٜىٰ كُواْ كُوَ يَسَاتَ عَڧَرْڧَشِنْ غَدُواْ؞ أَ مَيْمَكُوانْ حَكَ، ذَيْسَاتَ عَكَنْ سَنْدَا مَيْ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْ دَ ذَاسُ شِغَ سُغَ حَصْكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki, ko ya ajiye ta a ƙarƙashin gado. A'a, sai dai ya ɗora ta a maɗorinta, don masu shiga su ga hasken.