Luke 8:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُسَ دَ وُرِنَّنْ كُوَ أَݣَويْ وَنِ بَبَّنْ غَرْكٜىٰنْ أَلَدُنْ دَيَكٜىٰ كِيوُاْ أَغَنْ‌غَرٜىٰنْ تُدُنْ؞ سَيْ أَلْجَنُنْ سُكَ ضُواْڧِ عِيسَىٰ يَبَرْسُ سُشِغَ ثِكِنْ أَلَدُنْ؞ شِے كُوَ يَيَرْدَ مُسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, wurin nan kuwa akwai wani babban garkin alade na kiwo a gangaren dutse, suka roƙe shi ya yardar musu su shiga cikinsu. Ya kuwa yardar musu.