Luke 8:50 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ عِيسَىٰ يَجِ حَكَ، سَيْيَثٜىٰ وَ يَايِرُسْ «كَدَ كَجِڟُواْرُواْ، كَدَيْ بَادَ غَسْكِيَ، ذَاتَ سَاكٜىٰ رَايُوَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma da Yesu ya ji haka, ya amsa ya ce wa shugaban majami'ar, “Kada ka ji tsoro. Ka ba da gaskiya kawai, za ta kuwa warke.”