Malachi 1:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Edom zai iya cewa, “Ko da yake an ragargaza mu, ai, za mu sāke gina kufanmu.” Amma ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Za su iya gini, amma zan rushe. Za a ce da su Muguwar Ƙasa, mutane da kullum suke a ƙarƙashi fushin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كُواْدَيَكٜىٰ عٜىٰدُواْمَاوَا، وَتُواْ ذُرِيَرْ إِسُوَ، سُنْ ثٜىٰ، ‹أَنْيِ كَثَ كَثَ دَمُو، عَمَّا ذَامُ كُواْمَ مُسَاكٜىٰ غِنَا كُڢَنْمُ،› عَمَّا يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا يَثٜىٰ، ‹عِ، ذَاسُ غِنَا، نِے كُوَ ذَنْ رُشٜىٰ، حَرْ سَيْ أَنْثٜىٰ دَسُو مُوغُوَرْ ڧَسَا، مُتَنٜىٰنْ دَ ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ دَطٜىٰ عَكَنْسُ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.” Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”